Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi, da Ahmad Kabo Idris.
Dubban mutane a Venezuela na tsananin buƙatar abinci da matsuguni - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubban mutane na buƙatar abinci da matsuguni cikin gaggawa bayan tagwayen girgizar ƙasa da ta auku a Venezuela.
Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar ta ce ƙarancin abinci ya yi ƙamari, ayyukan yau da kullum sun tsaya cik, k...
