Wace ce Sadiya Farouq, ministar Buhari da EFCC ke nema ruwa a jallo?
A ƙarshen makon nan ne hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohuwar ministar jinƙai ta Najeriya, lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar ne bisa zarge-zarge ma...
